Rahotanni daga jihar sun ce yanzu an kara sassauta dokar inda za rika fita daga 6 na safe zuwa shida na yamma.
Ganin yadda a wasu wurare zanga zangar da ake ta hada da kada tutocin Rasha, kwararru sun fara kallon zanga zanga ta wasu sabbin fuskoki, a yayin da su kuma hukumomi ke kokarin sanin abin da hakan ke nufi.
Har yanzu ana ci gaba da zanga zangar nuna bacin rai game da tsadar rayuwa a Najeriya. A gefe guda kuma, masu fada a ji da sauran 'yan kasa na bayyana mabanbantan ra'ayoyinsu game da zanga zangar da kuma halayen wasu masu zanga zangar.
Dokar hana zirga-zirgar ta biyo bayan yadda aka ga wasu matasa da suka fito da sunan zanga-zanga, suna kewaye garin Jos da tutoci na kasar Rasha, suna barazana ga mutane da farfasa wasu shaguna da kwashe dukiyar jama'a a Bauchi Road da Zololo Junction da ke cikin kwaryar birnin na Jos.
Haka zalika an shawarci ‘yan Najeriya a Birtaniyar da su guji zuwa taron siyasa, zanga-zanga ko wani gangami da ke da mutane da yawa.
‘Yan Najeriya na ci gaba da nuna rashin gamsuwa da jawabin da Shugaba Tinubu ya yi a ranar Lahadi inda ya rarrashi ‘yan kasar da su kara hakuri kan halin da ake ciki
‘Yar wasan kwallon Kwandon mata ta Najeriya Ezinne Kalu ta yi nasarar samar wa kungiyar ta maki 21 kana Najeriya ta kafa tarihi ta bangaren maza da mata a gasar Olympics, inda ta zama kasar Afrika ta farko da ta isa wasan kwata fainal na kwallon kwando a wasannin Olympics.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed yayi jawabin kwantar da hankali da juyayin asarar rayuka da dukiyoyin gwamnati da al’ummar a zanga zangar da aka fara ranar 1 ga watan Agusta a sassa daban daban na Najeriya musamman a Arewa.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bukaci wadanda suka shirya zanga-zangar neman a kawo karshen tsadar rayuwa a kasa da su dakatar da duk wata zanga-zanga, domin kuwa kofar gwamnati a bude take a tattaunawa a kuma yi sulhu a samo hanyoyin kawo sauki a yanayin matsin da ‘yan kasa ke ciki a yanzu.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai yi jawabi ga al’ummar kasa kai tsaye a gobe Lahadi 4 ga watan Agusta, 2024, da misalin karfe 7 na safe agogon kasar.
“Muna tuhumar su da aikata laifuka da suka hada da tada hankali da jiwa jama’a ko jami’ai rauni ko lalata dukiya,” in ji CP Auwal.
Domin Kari