A yayin wata hira ta wayar tarho tsakaninsa da takwaransa na Najeriya, Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Oktoban da muke ciki, Biden ya bayyana aniyar inganta wakilcin nahiyar Afrika a tsarin Majalisar Dinkin Duniya.
Majalisar Dokokin jihar Nejan dai ta bukaci Gwamnatin jihar da Hukumar Sojin kasar da su yi duk mai yiwuwa domin kwato wannan daji na horar da sojojin daga hannun 'yanbindigar.
Gwamnatin jihar ta Kano ta ce sabon albashin zai fara aiki daga watan Nuwambar 2024.
Shugaba Joe Biden na Amurka ya jajanta game da iftila’in ambaliyar ruwan baya-bayan nan da ta shafi yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Dangote, wanda ke jawabi ga manema labaran fadar gwamnatin Najeriya a Abuja, ya bukaci kamfanin man Najeriya (NNPCL) da dillalan man dake fadin kasar su dakata da shigo da man daga ketare.
Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin gaggauta aikin gyara domin dawo da hasken lantarki ga shiyar arewacin Najeriya.
An kama wadanda ake zargin ne a wani wurin hakar ma’adinai ta barauniyar hanya dake yankin Rafin-Gabas, Agwada, a karamar hukumar Kokona ta jihar.
Kamfanin fasahar hada-hadar kudi na Moniepoint mai tushe a Najeriya ya tara dala miiyan 110 daga kudaden da masu zuba jari ciki harda kamfanin Google suka zuba da nufin bunkasa hada-hadar kudin na’ura da samarwa harkar bankin mafita a fadin Afrika, a cewar Moniepoint a yau Talata.
Bangaren sojin sama na aikin wanzar da zaman lafiya na “Operation Hadin Kai” ya hallaka dimbin ‘yan ta’adda a yankuna 2 na garin Bula Marwa dake jihar Borno.
Yanzu dai kimanin makonni biyu kenan babu hasken wutar lantarki a daukacin yankin na arewacin Najeriya birni da karkara.
Yanzu dai da wannan hukuncin na kotun daukaka kara karo na biyu, kotun koli ce kawai ta yi saura ta yi nata hukunci a kan karar.
Madrid da 'yan wasanta baki daya ba su halarci bikin ba, sannan sun shiga shafukan sada zumunta sun rubuta kalaman da suka nuna bacin ransu saboda ba a zabi Vinicius Jnr ba.
Domin Kari