Hambararren shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum ya cika watanni uku a tsare tare da mai dakinsa da dansa, tun bayan da sojoji suka kifar da gwamnatinsa a ranar 26 ga watan Yuli, lamarin da ya sa har yanzu makomarsa ke cikin rashin tabbas.
Kungiyar UNESCO ta ce Afirka na ci gaba da fuskantar kalubalen karancin malamai a makarantu da dama sakamakon Karin masu nemar illimi sannan, da karancin wadatattun kayayyakin aikin da za su taimaka wajen inganta fannin illimi.
Amurka ta dakatar da galibin tallafin kudi ga kasar Gabon da ke tsakiyar Afirka a matsayin mayar da martani ga juyin mulki da sojoji suka yi a watan Agusta.
A Nijar, wasu kungiyoyin farar hula sun kafa hadaka mai lakanin DCTR da nufin taimaka wa gwamnatin sojan kasar a yunkurin neman mafita sakamakon takunkumin kungiyar CEDEAO, suna masu jaddada aniyar bada gudummowa a dukkan tsare tsaren da suka shafi yunkurin mayar da kasar kan turbar dimokradiyya.
Lauyoyin da ke kare hambararren shugaban Nijar Mohammed Bazoum sun maida martani ga gwamnatin mulkin sojan kasar wace ta zarge shi da yunkurin tserewa daga inda ake tsare da shi tsawon watanni kusan uku, inda suka bukaci mahukuntan na Nijar su gaggauta sakin shugaba Bazoum da iyalinsa .
Bankin Duniya ya sanar da cewa, sama da kashi ɗaya bisa huɗu na 'yan Ghana suna rayuwa ne a kasa da dala $2.15 (GHS 25.31) kowace rana, wato kimanin 'yan Ghana miliyan 7.7 ne ke nan.
Sojojin da suka yi juyin mulki ranar 26 ga watan Yulin 2023 a Jamhuriyar Nijar sun sanar da dakile wani yunkurin arcewar hambararren Shugaban kasa Mohamed Bazoum da iyalinsa daga inda ake tsare da su.
Kimanin mutum 20,000 ne ibtila'in ambaliyar ruwa ta tilastawa barin gidajensu a yankin kudu maso gabashin kasar Ghana da wasu matsugunai a birnin Accra da ma jihar gabashin kasar.
A Jamhuriyar Nijar wasu kungiyoyin mata sun yi zaman dirshan a harabar ofishin CEDEAO na birnin Yamai da nufin jan hankalin shugabanin kungiyar da su janye takunkumin da suka sanya wa Nijar sanadiyar juyin mulkin ranar 26 ga watan Yuli.
An yankewa wasu ‘yan barandan siyasa 16 na jam'iyyar NPP mai mulki hukuncin tarar Ghana Cedi 2,400 (wato kimanin $200) ga kowannensu, domin kutsawa da suka yi cikin shirin talabijin da ke gudana kai tsaye.
Hukumomin tsaron Jamhuriyar Nijer sun bada sanarwar kashe gomman ‘yan ta’adda yayinda sojoji 6 suka rasu wasu 18 suka ji rauni sakamakon gumurzun da aka yi a arewacin jihar Tilabery.
A wani yunkurin samar da kudaden daukar dawainiyar al’amuran gudanar da sha’anin mulkin gwamnatin rikon kwaryar Jamhuriyar Nijar, gwamnatin mulkin soji ta kafa wata gidauniya da nufin tattara gudummawar kudade daga ‘yan kasar na ciki da waje.
Domin Kari