Alkaluman zaben sun nuna cewa Deby Itno ya samu kashi 61 cikin 100 na kuri’un da aka kada, yayin da Masra ya samu kashi 18.5.
A cewar rahoton, adadin mutanen da zasu fuskanci matsalar karancin abinci a yankunan yammaci da tsakiyar nahiyar afirka a wannan dan tsakani zai kai kimanin mutane milyan 52 kwatankwacin kaso 12 cikin 100 na mutanen da aka tantance.
A ranar Juma’a ne likitoci a Kenya za su koma bakin aikin su, bayan sun amince da gwamnatin a kan yadda za a biya su sauran albashinsu da ya makale.
Shugaban kasar Kenya William Ruto ya ayyana Juma'a a matsayin ranar hutu domin makokin mutane 238 da suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da ake ci gaba da yi.
An kiyasta cewa ana samun asarar dala tiriliyan 3.6 a tattalin arzikin duniya a shekara, a sanadiyar harkokin da suka danganci cin hanci da rashawa.
Shugaban na Senegal ya zabi a shiga filin jirgin saman ba tare da wani kace-nace ba. Ba wani jerin gaishe-gaishe ko wani biki. Da ga shi sai abokan tafiyar sa kawai.
Gwamnatin ta dauki wannan matakin ne na rufe wuraren hakar ma’adinan zinare dake arewacin kasar bayan da wasu dabbobi suka mutu sakamakon shan ruwa mai dauke da guba a wurin.
A watan Mayu ne ya kamata a fara jigilar danyen man Nijar daga tashar jirgin ruwan Seme a jamhuriyar Benin zuwa kasuwannin duniya, gwamnatin shugaba Patrice Talon ta yanke shawarar hana gudanar da wadannan ayyuka da nufin maida martani ga mahukuntan Nijar da ke ci gaba da rufe iyakar kasar.
Bakin haure akalla 107 da suka hada da mata da yara da ke garkame ne aka kubutar a wani gari da ke kudu maso gabashin kasar Libya, kamar yadda wani mai magana da yawun hukumar tsaron kasar ya sanar a ranar Litinin.
A ranar litinin ake kammala zaben shugaban kasar Chadi inda fararen hula suka fita rumfunan zabe, kwana daya bayan da sojoji suka kada kuri’unsu. Shugaban rikon kwarya Janar Mahamat Idriss Deby dai na fuskantar kalubale guda tara da suka hada da firaministan sa na yanzu.
Rukunin sojojin Rasha na biyu ya isa jamhuriyar Nijer wadanda aka ayyana a matsayin masu aikin horo a ci gaba da karfafa huldar aiyukan soja a tsakanin kasashen biyu bayan juyin mulkin da ya hambarar da shugaba Mohamed Bazoum.
Domin Kari