Daruruwan al-umma sun yi dafifi domin nuna farin cikinsu bisa haifan da na miji, da mai dakin Yarima Williams tayi ran Litinin dinnan.
Sojoji sun hambarar da shugaban demokradiyya na farko a kasar Masar, kuma sun rantsar da shugaban rikon kwarya yau kwana daya kennan, kuma wannan lamari, ya samu tsokaci iri-iri daga manazarta da kwararru a harkokin siyasa.
A Nijar-rikicin jam'iyar CDS bangaren mahaman usman yace zai daukaka kara a gaban kotun CEDEAO ko ECOWAS.
Wata tawagar manyan jami’an kungiyar hada kan kasashen larabawa, ta bayyana goyon baya ga manufofin shawarwari tsakanin Isra’ila da Falasdinu.
Babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniyar ya ce za a bukaci rundunoni biyu daban-daban a kasar Mali, rundunar mayaka da ta kiyaye zaman lafiya
Kamfanin dillancin labaran kasar Mauritania ya ce al-Qaida ta kashe dan kasar Faransar da ta ke yin garkuwa da shi a kasar Mali
Hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka, NASA, ta ce na’urar ta, ta Curiosity ta samo wata shaida mai nuna cewa an yi rayuwa a duniyar Mars.
Faransa ta ce za ta yi iyakacin kokarin ta na ganin ta kubutar da 'yan kasar bakwai da aka sace a kasar Kamaru ana yin garkuwa da su
Karshen ta dai Chuck Hagel ya zama sakataren tsaron Amurka duk da kokarin da wasu 'yan Republican su ka yi na neman hana tabbatar da shi
Mataimakin shugaban kasar Venezuela ya ce shugaba Hugo Chavez na cikin wata jinya mai sarkakkiya a kasar Cuba
Domin Kari