Yayin da darajar Naira a Najeriya ta yi mummunar faduwa, ‘yan kasuwa na kokawa da tsadar dala, mutanen gari kuma na kokawa da tsadar kayan masarufi, da wasu rahotanni
Kimanin yara miliyan ashirin ne aka kiyasta ba sa zuwa makaranta a Najeriya wani lamari da kwararru suke ta’allakawa akan matsalolin al’adu, da tattalin arziki da kuma rashin makarantu na kwarai da wa su rahotanni
Wasu daga cikin kurakuren da marasa lafiya ke samu a wajen duba lafiyarsu a Najeriya, ana danganta su ne da rashin kwarewar jami’an lafiya ko kuma shagunan magani na cikin unguwa, da wasu rahotanni
Labarin sace kodojin mutanen ya jefa mutane da dama da aka taba yi musu aiki a asibitin cikin rudani, yayin da wasun su ke zuwa ana duba su ko suma an sace musu na su kodojin.
A birnin Kirkand na jihar Washington a Amurka, masu zanga-zangar goyon bayan Isra’ila da na Falasdinawa, sun so su ba hammata iska, yayin da suka fita kan tituna dauke da tutocin bangarorin da suka marawa baya, da wasu rahotanni
Mohammad Qaddam Sadiq Isa, wani mai bincike da sharhi a kan harkokin Gabas ta Tsakiya wanda yake zaune a Dubai ya mana karin haske akan rikicin da ke tsakanin Isra’ila da Falasdinawa, mai dadadden tarihi da ya ki ci ya ki cinyewa
Domin Kari