Fadar shugaban Najeriya tace ta biyo bayan bankado ma’aikatan bogi da tayi, yanzu an toshe kofar wawure Nairan Biliyan 13 a duk wata.
Ana tuhumar tsohuwar shugabar kasar Argentina, Cristina Fernandez da laifukan cin hanci da rashawa, inda ta ba da umurnin a boye wasu miliyoyin kudade.
Wani tsohon jami’in kasar Korea ta Arewa da ya sauya sheka zuwa Korea ta Kudu, ya ce shekara mai zuwa, za ta ba da babbar dama ga gwamnatin Korea ta Arewan, wajen bunkasa shirinta na nukiliya.
Turkiyya da Rasha sun cimma wata sabuwar matsaya kan shirin tsagaita wuta a Syria, kuma suna kan aiki dangane da yadda wannan matsaya za ta fara aiki a daren yau Laraba.
Gwamnatin Najeriya na yin aniyar juya sansanin da ta kwace daga hannu Boko Haram a dajin Sambisa da akafi sani da ‘Camp Zero’ zuwa cibiyar soja don lamuran dabarun yaki da gwajin makamai a dajin.
Fitacciyar ‘yar wasan kwaikwayon Amurka, Carrie Fisher mai fitowa a fina-finan "Star Wars" ta rasu ta na mai shekaru 60.
‘Yan adawa a babban birnin Yamai sunyi suka da kakkausar murya ga majalisar matasa ta jamhuriyar Nijar, kan cewa ‘ya ‘yan masu kudi da mulki ne kadai ke cikin majalisar.
Gwamnan jihar Borno da babban hafsan sojan ‘kasa na Najeriya sun sake bude wasu manyan hanyoyi a jihar Borno wadanda dukkanninsu ke da iyaka da kasar jamhuriyar Nijar.
Jami’ai sun ce, Kusan mutane biyu ne suka mutu sakamakon Mahaukaciyar guguwar Nock-Ten, wacce ta birkita shagulgulan kirsimeti a wani sashi na kasar Philippines, guguwar da ta saukar da Iska da Ruwa a Manila a yau Litinin.
Masana na gargadin yiwuwar samun yakin sari-ka-noke daga mayakan Boko Haram biyon bayan fatattakarsu da rundunar sojan Najeriya tace ta yi daga sansaninsu na ‘karshe a dajin Sambisa.
A kalla mutane biyu ne suka rasa rayukansu biyo bayan rugujewar wani ginin ma’aikatar ‘yan sanda a yankin Ikeja dake tsakiyar birnin Lagos.
Domin Kari