Shugabannin kasashen duniya sun sanar da takwarorinsu matsaloli da kuma manufofinsu; Dalilai da ya sa manufofin da ake cimmawa a wajen irin wannan taro ba sa kai labari; Manufar da hukuncin kotun kararrakin zabe a jihar Kano ke nunawa, da wasu rahotanni
Bayani kan yadda shugabannin kasashen duniya suka gabatar da jawabai da suka tabo batutuwa daban-daban a wurin babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 da ya gudana a birnin New York na Amurka
Gwamnatin Kenya na samar da matsugunai ga wadanda suka tsira daga safarar mutane; Ficewar Rasha daga yarjejeniyar fitar da Hatsi ta Bahar Maliya na shafar kokarin Najeriya na dogaro da kai, da wasu rahotanni
Kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afirka ECOWAS ta dauki matakin kakabawa jamhuriyar Nijar takunkumi tare da baiwa jagoran mulkin wa’adin kwanaki bakwai ya mika mulki ga gwamnatin farar hula.
A kwanakin baya ne ministan 'yan sandan Afirka ta Kudu Bheki Cele da tawagar manyan jami'an 'yan sanda suka dawo daga ziyarar da suka kai kasar China, inda suka tattauna kan karfafa hadin gwiwar tabbatar da doka da oda.
Jami'an kiwon lafiya na Falasdinu sun fada ranar Alhamis cewa sojojin Isra'ila sun harbe wani Bafalasdine a yammacin gabar kogin Jordan da suka mamaye.
Kungiyar agaji ta Mercy Corps ta ce fada da ake ci gaba da yi a Sudan na iya janyo mummunar matsalar abinci. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugabannin kasashen gabashin Afirka suka ce suna shirin ganawa da masu ruwa da tsaki a fadan Sudan don samar da masalaha.
An yanke wa wata mata ‘yar shekaru 44 hukuncin daurin shekaru sama da biyu a gidan yari a kasar Ingila ranar litinin, bisa samun ta da laifin zubar da ciki kimanin watanni takwas da daukar cikin.
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump, ya isa kulob din Golf dinsa da ke birnin Miami gabanin gurfanar da shi a gaban kuliya bisa zarginsa da laifin karkatar da wasu bayanan sirrin tsaron kasar bayan ya bar fadar White House a shekarar 2021.
Dubban 'yan gudun hijirar Sudan da suka tsere zuwa kasar Chadi domin gujewa fada a kasarsu na iya fuskantar katsewar tallafin jin kai da magunguna yayin da damina gabatowa, in ji kungiyar agaji ta Medecins Sans Frontieres (MSF).
Domin Kari