A wani matakin tunkarar kalubalen tsaro da ya ke naso a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya da ma wasu jihohi bakwai da ke makwabtaka da ita, mahukunta sun kaddamar da wani shirin kawo karshen matsalar.
Hukumar dake kula da ayyukan yansandan Najeriya ta kori wasu manyan ‘yan sanda bakwai daga bakin aiki tare da rage mukaman wasu ‘yan sandan.
Rundunar sojojin Najeriya ta ja kunnen masu rura wutar rikici a sassa daban daban na kasar da su yiwa kansu kiyamullayli, domin kuwa rundunar zata dau duk wani matakin da ya dace kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya bata wajen ganin ta kare yan kasa na gari.
Ana zargin farfesa Zainab Dinne da wata mai mata aikin gida Rebecca Enechido da kuma wani mutum da laifin cin mutuncin 'yar sandar da raunata ‘yar sanda mai tsaron lafiyarta.
Jiragen yakin sojojin saman Najeriya sun yi luguden wuta a sansanonin hatsabinin dan bindigar nan Bello Turji su ka kashe mutanensa da dama.
Yayin da hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya ta DSS ta nemi wata babbar kotun tarayya ta ba ta damar ci gaba da tsare mawallafin jaridar Desert Herald Mallam Tukur Mamu har tsawon kwanaki 60, lauyoyin Mamu sun ce babu abun fargaba gaskiya z ata yi halinta.
Jami'an hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya ta DSS sun kai wani samame a gidan surikin mawallafin jaridar Desert Herald Mallam Tukur Mamu da tsakar daren ranar Alhamis inda suka yi awon gaba da shi zuwa ofishinsu.
Malam Mamu ne ya shiga tsakani wajen karbo kusan mutum 20 daga cikin fasinjojin jirgin kasa da ‘yan bindiga suka sace a watan Maris din wannan shekara.
A baya, ya taba shaidawa Muryar Amurka cewa ya janye daga shiga tsakani a kokarin kubutar da sauran fasinjojin jirgin kasa da aka sace, saboda abin da ya kira barazana da rayuwarsa take fuskanta.
Hafsan hafsoshin sojin Najeriya Laftanar Janar Faruk Yahaya ya bayyana cewa, za a yi amfani da dokar kasa wajen hukumta sojan da ya kashe limamin addinin Islama a jihar Yobe
Yayin da lamarin tsaro ke ci gaba da ta’azzara a wasu sassan Najeriya, rundunar mayakan ruwa na taka muhimmiyar rawa wajen ganin an samar da zaman lafiya a ciki da wajen kasa.
A ci gaba da samun nasara da sojojin Najeriya ke yi a baya bayan nan, dakarun Operation Hadarin Daji da ke aiki a arewa maso yammacin Najeriya, sun damke wasu miyagu da su ka shigo daga kasashen ketare.
Hedkwatar tsaron Najeriya ta ce an sake damko karin wasu yan ta'adda guda biyu dake cikin maharan da suka kai harin cocin Owo
Shi dai wannan kwamanda na Boko Haram shi ne wanda a shekarar 2014 ya jagoranci kai farmakin da ya yi sanadin kashe daruruwan mutane a garin Bama tare da maida garin karkashin ikon abin da suka kira Daularsu
Kusan kashi saba'in cikin dari na mutanen da ake safara zuwa Jamhuriyar arewacin Cyprus ‘yan mata ne daga Najeriya kuma suna karewa ne cikin ayyuka da ke da alaka da nau'ikan bauta.
Hedkwatar tsaron Najeriya tayi watsi da zargin cewa sojoji na kitsa juyin mulki don hambarad da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Amurka da Burtaniyan sun fidda takardun gargadi ga yan kasashen nasu biyo bayan mummunan harin ta'addanci da aka kai gidan gyaran hali na koje dake yankin babban birnin Tarayyar Najeriya
Shugaban Najeriya ya kai ziyarar gani da ido gidan gyaran halin Kuje cikin wani farin jirgi mai saukar angulu, ya dudduba wuraren da 'yan ta'addan suka dagargaza.
Bayanai daga yankin tafkin Chadi na nuna cewa jiragen yakin rundunar dakarun kawancen kasashen yankin sun kaddamar da wani babban farmaki a kan ‘yan ta'addan kungiyar ISWAP inda suka hallaka da yawa daga cikinsu.
Domin Kari