A cikin shirin wannan makon tun bayan da Faransa ta sanar da shirinta na janye dakarunta a yankin Sahel na Afirka, jama’a a Mali da Chadi da Nijar ke ta tsokaci game da tasirin wannan mataki akan yaki da ‘yan bindiga masu da’awar jihadi, da wasu rahotanni.
A cikin Shirin na wannan makon yayin da ake ci gaba da samun hadarin jiragen ruwa a wasu sassan Najeriya, wasu al’ummomi a jihohin Kebbi da Sokoto sun bukaci gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su sa hannu don kawo karshen asarar rayuka da dukiyoyi, da wasu sauran rahotanni.
A cikin shirin na wannan makon tun bayan da shugaban kasar Najeriya ya sanar da nadin Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon babban hafsan sojin kasar, ‘yan kasar ke ci gaba da tsokaci a game da irin aikin dake gaban sabon babban hafsan sojin, musamman batun Boko Haram da wasu sauran rahotanni.
A cikin shirin na wannan makon a birnin Jos dake Najeriya wata kungiya mai zaman kanta ta dukufa wajen wayar da kan mutane don kaucewa furta kalaman kiyayya dake haddasa munanan rikice-rikice a tsakanin al’umma, da wasu sauran rahotanni.