A Nijar, inda aka samu juyin mulki sannan aka kakaba wa kasar jerin takunkumai, ayyukan kungiyoyin jinkai ya ragu sossai, lamarin da ya jefa al’ummomin da suke ba su tallafi cikin takaici.
Karancin kwararrun ma'aikatan kiwon lafiya na shafar hanyoyin samun kulawar mutane, da ingancin kulawar da suke samu, da kuma yawan mutanen dake mutuwa sakamakon cututtuka a nahiyar.
Akan dambarwa dake faruwa a Nijar, mun samu tattaunawa da jakadan Nijar din anan Amurka, Mamadou Kiari Liman-Tinguiri, mun kuma duba taron gaggawa da Kungiyar ECOWAS ta yi a Abuja, Najeriya, da wasu rahotanni.
Halin matsin tattalin arziki a Najeriya sakamakon cire tallafin man fetur ya sa hukumomin yin kokarin bunkasa amfani da wasu hanyoyin makamashi da ba na fetur ba, abin da ya hada da canza injuna zuwa masu aiki da iskar gas da fadada tashoshin cajin motoci masu amfani da lantarki, da wasu rahotanni
Kwararru sun ce ana samun karuwar mutane masu kananan shekaru tattare da cutar bugun jini a fadin duniya sannan wasu dalilai da suke haifar da wannan yanayi sun hada da kiba mara kima, hawan jini da kuma cutar sukari wato diabetes.
Yayin da 'yan Najeriya ke ci gaba da kokawa da tsadar kayan masarufi, a makon jiya 'yan majalisar dokokin kasar suka amince da bukatar shugaba Bola Tinubu ta ciyo bashin dala miliyan 800 daga bankin duniya don taimakawa wajen rage radadin cire tallafin man fetur, da wasu rahotanni
Bisa binciken cibiyar kiwon lafiya ta Amurka, samun isashen bacci yana inganta yadda kwakwalwa take aiki, yanayin farin ciki da kuma lafiyar ka. Rashin sammun wadatacen bacci na kara barazanar kamuwa da cututtuka da matsalolin lafiyar jiki.
Illolin matsalar wutar lantarki a Najeriya ba su tsaya kawai ga hana ci gaban tattalin arziki ba, har ma da bangaren kiwon lafiya; haka kuma hukumomin Ghana su na shirin kaddamar da wata tashar samar da wutar lantarki daga hasken rana da aka gina akan madatsar ruwa da wasu rahotanni
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce matsananciyar damuwa mai alaka da aikin da mutun ke yi, ta na samuwa ne sakamakon irin yanayin aikin da mutun ke yi, ko kuma yanayin da ya ke yin aikin, ko jadawalin aikin na shi ko kuma rashin samun damar karin girma ko cigaba a wurin aiki.
Barkewar cutar Anthrax dake kama dabbobi har ma da mutane na ci gaba da haifar da damuwa a kasashen yammacin Afirka. A cewar Cibiyar Kula da Cututtuka ta Afirka, ana iya samun cutar anthrax a cikin dabbobin daji da na gida kamar shanu, awaki, dawakai, da barewa.
A makon da ya gabata ne Kotun Kolin Amurka ta yanke hukuncin hana amfani da tsarin ware wasu guraben daukan dalibai a jami’o’i bisa launin fatar dalibai, da wasu rahotanni
Mustapha Yahuza Umar, Kwamandan Hukumar NDLEA a Jihar Plateau, ya yi mana karin haske kan tattaki na wayar da kan mutane musanman matasa a game da haduran miyagun kwayoyi da hukumar ta yi.
Wasu mutane mazauna birnin Jos sun bada ra’ayoyinsu game da matsalar miyagun kwayoyi, a inda suke da kuma irin taimakon da yakamata a baiwa masu ta’ammali da kwayoyi.
A Najeriya, talauci shi ne babban dalilin da ke sa yara da dama ba sa zuwa makaranta, sai dai ana kara kokarin ganin an magance wannan matsala, yadda Musulmai suka gudanar da Idin babbar Sallah, da kuma wasu rahotanni
A birnin São Paulo na Brazil, wata sabuwar kwayar da ake yi da sinadari ta na daure kan hukumomi. Ana kiran kwarar da suna K9, kuma ta na da rahusa sosai, sannan ta na zamewa masu shanta jaraba.
Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun bukaci hukumomin Najeriya da su dakatar da shirin mayar da ‘yan gudun hijira garuruwansu a arewa maso gabashin kasar, da wasu rahotanni
Bisa kididdigar da hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar, kusan dukkan mutane a duniya suna shakar iskar da ta zarce ka'idojin ingancin iska na hukumar lafiya ta duniya – wato isa da take a gurbace. Wannan gurbacewar yanayi na da illa ga lafiyar dan adam.
Yajin aikin da masu dafa abinci a makarantu ke yi na iya tilasta wa yaran makaranta da ke cin gajiyar shirin ciyar da dalibai da gwamnatin Ghana ta bullo da shi zama da yunwa, da wasu rahotanni
Ana samun ciwon ne sakamakon doguwar nakuda yayin da da yake yunkurin fitowa, inda kuma mahaifiyar ba ta samun kulawar gaggawa da ta dace a asibiti.
Tun bayan ayyana cire tallafin man fetur kawunan ‘yan Najeriya ya rarrabu, yayin da wasu ke goyon baya, wasu na sukar matakin, saboda su na ganin zai shafi da dama daga cikin marasa galihu da ke fama da matsin tattalin arziki, da wasu rahotanni
Domin Kari