Ministan yada labarai na Najeriya, Mohammed Idris ya yi tsokaci a game da tasirin sashin Hausa na Muryar Amurka.
A ci gaba da shagulgulan cikar VOA Hausa shekara 45 da kafuwa, ma’aikatan shashin a Washinton DC sun gudanar da ‘yar kwarya-kwaryar liyafa, wacce ta samu halartar baki daga Amurka da wakilan ofishin jakadancin Najeriya a Washington.
Ministan Zongo a Ghana, Ben Abdallah Banda ya tsokaci a game da cikar Muryar Amurka shekara 45 da kafuwa.
Duk da matakai da ake cewa ana dauka don samar da tsaro, ana ci gaba da samun matsalar satar mutane don kudin fansa a wasu sassan kasar, ciki har da Abuja babban birnin tarayyar kasar.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayana cewa kasar Cape Verde ta yi nasarar kawar da cutar Malariya. Kasar ta zama ta 3 a nahiyar Afirka da aka tabbatar da nasasrar kawar da cutar bayan kasar Mauritius a shekara ta 1973 da Algeriya a 2019.
Shirin Taskar VOA na wannan makon, shiri ne na musanman da Muryar Amurka ta hada a game da yaki ko tashin hankali da ake fama da shi a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, da kuma mawuyacin hali da mutane ke ciki sakamakon rikicin.
Waiwayar wasu daga cikin manyan al’amura da suka faru a wannan shekara mai karewa, ciki hadda rantsar da shugaba Bola Tinubu a matsayin shugaban kasar a Mayu, da kuma cire tallafin man fetur da ya kara tsananin rayuwa a tsakanin jama’a.
Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta ce ba ta gamsu cewa sojojin Najeriya za su gudanar da irin bincike na gaskiya ba a game da harin da sojoji suka kai a kauyen Tudun Biri a Kaduna, wanda ya halaka sama da fararen hula 100.
Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta bayyana muhimmancin lafiya da cikakken lafiyar jiki, na kwakwalwa da kuma mu’amala da mutane, kana hakan baya nufin rashin lalura gaba daya.
Hira da Zaliha Lawal, Darektar shirin cibiyar Connected Development da aka fi sani da CODE a game da kasafin kudin 2024 da shugaban Najeriya Tinubu ya gabatar a majalisar tarayyar kasar a kwanan nan, inda ta tabo batun tattalin arziki da harkokin kiwon lafiya.
Domin Kari