Ukraine ta kai wani babban hari a birnin Moscow a ranar Laraba tare da harbo jiragen sama mara matuka guda 11 da jami'an tsaron kasar Rasha suka ce na daya daga cikin hare-hare mafi girma na jirage marasa matuka akan babban birnin kasar tun bayan yakin na Ukraine da aka fara a watan Fabrairun 2022.
Hukumomin mulkin sojan Burkina Faso, Mali da Nijar sun rubutawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya wasika domin yin Allah-wadai da zargin goyon bayan da kasar Ukraine ke yi wa kungiyoyin 'yan tawaye a yankin Sahel da ke yammacin Afirka, kamar yadda kwafin wasikarsu ta nuna.
Wata motar bas mai dauke da alhazan Shi'a daga Pakistan zuwa Iraqi ta yi hatsari a tsakiyar kasar Iran, inda akalla mutum 28 suka mutu, a cewar wani jami'i a ranar Laraba.
Jam’iyyar Democrat ta fara babban taronta na kasa a ranar Litinin a Chicago inda ake sa ran kusan mutum 50,000 za su isa birnin.
Hukumomin lafiya a kasar Sudan sun sanar a ranar Lahadi cewa cutar barkewar cutar amai da gudawa ta yi sanadin mutuwar mutane kusan dozin biyu tare da jikkata wasu da dama.
Zanga-zangar Kenya ta yi tasirin da ‘yan zamanin Gen Z suka tilastawa shugaban kasar rusa majalisar ministocinsa; Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin kimanin dala miliyan 30 don inganta wani gandari a Birnin N'Konni a Nijar; Tarihi da tasiri mataimakan shugabannin Amurka da wasu rahotanni
Domin Kari