Shugaba Cyril Ramaphosa ya yi wa majalisarsa garanmbawul ciki har da sake nada Nhlanhla Nene da Jacob Zuma ya kora a matsayin ministan kudi.
Majalisar dinkin Duniya ta lura cewa ya zama tilas a kwashe mutane a gabashin Ghouta saboda fada ada ake ci gaba da yi, duk da cewa akwai yarjejeniyar tsagaita-wuta ta sao’I biyar da shugaba Bashar al Assad ya ayyana.
Injiniyoyi matasa na ba da himma wajen kera jirage marasa matuka, saboda wani shiri na shata taswirar birnin Duala ta yadda za a iya hango bala’o’i nan take a kuma yaki masu farauta ba izini.
Jama’ar Agadez sun kwashe kwanaki uku a wajen bulbular IFEROUNE domin gudanar da bikin de L’Air da nufin bunkasa harkar yawon bude ido.
Jami’an tsaron gabar teku sun ceto bakin haure 441 yayin da kwalekwalensu ya saki hanya daga yammacin gabar teku.
Kungiyoyin Masu aikin ceto na neman wadanda suka rayu, bayan wani jirgin saman fasinja ya fadi cikin tsaunukan Zagros, dake kasar, ana kyautata zaton mutane sama da 60 sun mutu.
Shugaba Adama Barrow ya dakatar da dokar hukuncin kisa, da zummar soke ta gabaki daya a lokacin jawabinsa na zagayowar ranar samun ‘yancin kai a Banjul
Domin Kari