Yan sandan kasar Malaysia, suka kai samame a gidan tsohon firayin minista Najib Razak, a yayin da yake fuskantar sabaon bincike akan cin hanci da rashawa da wadanda suka kada shi zaben da aka gudanar kwanan nan ke jagoranta.
Shugaba Donald Trump da mataimakinsa Mike Pence sun tarbi wasu Amurkawa 3 da aka sako daga Koriya ta Arewa a Washington.
Firayin ministan kasar Mali Soumeylou Boubeye ya kai ziyara garin Menaka dake iyakar kasar da Nijar, inda aka yi mummunan tashin hankali kwanan nan.
Duniya: Shugaban Amurka Donald Trump ya yi sanarwar janyewa daga yarjejeniyar nukiliya da Iran amma sauran kasashen da ke ciki ba su janye ba.
A Najeriya Shugabanni na halartar taron tafkin Chadi a Maiduguri domin tattauna makomar yankin don kawo ci gaba.
MALI: Shugaban jama’iyya mai mulki ya fadawa daruruwan magoya bayan su a Bamako cewar shugaban kasa Ibrahim Boubacar Keita yana son tsayawa takara karo na biyu.
RUSSIA: Yau litini aka rantsar da Vladimir Putin wanda kodai shugaban kasa ne ko kuma Firayin minsitan kasar Rasha tun shekarar 1999, a karo na hudu.
Sudan ta Kudu, ministan harkokin wajen kasar Masar Sameh Shoukry tare shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni suka halarci babban taro na musamman a kasar Juba da shugaba Salva Kiir, kafin a fara taron tattaunawa na wanzar da zaman lafiya.
Gwamantin kasar Amurka ta ci alwashin dorawa kasar china alhakin amfani da wutar laser a kusa da sansanin dakarun kasar Amurka dake Djibouti da ya yi sanadiyar yiwa wasu matukan jiragen yakin amurka biyu rauni. Zarginda kasar China ta musanta.
Domin Kari