‘Yar raji, kuma fitacciyar shugabar hadakar jam’iyyun adawa Dr. Isatou Touray, na da kwarin gwiwar cewa hadakar tasu za ta yi nasara a zaben shugaban kasa da za a yi ranar Alhamis.
Kasar Cuba na cikin makoki na tsawon kwanaki na juyayin tsohon jagoran juyin-juya-halin kasar, Fidel Castro, wanda ya rasu ranar Jumma’ar da ta gabata yana da shekaru 90.
A cikin shirin namu na yau za ku ga yadda harkar sayar da tsofin karafuna ke tsabtace mahalli tare da samar da kudaden shiga ga matasa.
UAE/Nigeria: Makarantar Makoko dake yawo akan ruwa a Lagas Najeriya, ta samu matsayi na 19 a wajen bikin zane na Aga Khan da aka yi a Dubai.
Sama da mutane 5000 ne suka yi zanga zangar nuna rashin jin dadin da zargin kisa da fyaden da ake wa Musulmi ‘yan kabilar Rohingya a Myanmar.
Kotun soju ta musamman a Maiduguri ta yanke hukumci kan wasu sojoji
Kotun soji ta musamman a Maiduguri ta yanke hukumci kan wasu sojoji, Nuwamba 25, 2016
Babbar kotun sauraren manyan laifuka ta Birnin Konni a karkashin kotun daukaka kara ta babban Birnin Niamey ta soma taron ta na shekara shekara a garin Birnin Konni inda zata duba laifuka 32 da suka shafi kisa, fiyade da kashe yara sabin haihuwa.
Dakarun saman Najeriya sun ce sun kai hare-haren sama a maboyar kungiyar Boko Haram inda suka kashe da dama daga cikin mayakan.
Mayakan Houthis da Kawayensu sun hada wani faretin soja a Amran, wani gari dane hannun 'yan tawayen Shi'a dake fada da fgwamnatin kasar wanda Saudi ke goyon baya.
A wani hoton bidiyon na Yotube, zababben shugaba Donald Trump, ya ce Amurka za ta janye daga yarjejeniyar kasuwancin nan ta TPP da ta kulla da wasu kasashe.
Wani basaraken Najeriya ya bayyana a kotu, inda lauyoyi suka neman kamfani Shell na kasar Holland ya share man da ya kwarara wanda ke lalata muhalli.
Babban hafsan hafsoshin Nijeriya Janar Abayomi Olonishakin, yace kofarsu a bude take domin karbar bayanan da zasu basu damar chafke 'yan kungiyar Boko Haram din da ake nema.
Paparoma francis ya rufe hidimar ibada ta “Shekara Mai Tsarki ta Jinkai” ta Cocin Katolika ranar Lahadi a wata liyafar da aka yi a babbar Majami’ar St. Peter’s Basilica, inda Paparoman ya rufe “Kofarsa Mai Tsarki.”
An fara kada kuri’ar zaben kananan hukumomi a Mali, sai dai an ce babu jama’a sosai yayinda kasar ke fuskantar rashin zaman lafiya da kuma dokar ta baci da aka kafa.
Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada aniyarta na marawa gwamnatin Najeriya baya kan yakar 'yan Boko Haram.
A Cikin shirin namu na yau, zaku ga cewa nasarar bazata da Donald Trump ya samu a zaben Amurka ta haddasa zanga-zanga a duk fädin kasar, inda jama'a ke nunan rashin amincewar su da wasu daga cikin ra'ayoyin shi.
Domin Kari