A yayin ziyarar da mataimakin babban sakataren Majalisar Dinki Duniya, MDD mai kula da ayyukan jinkai da ba da agajin gaggawa ya kai a sansanin 'yan gudun hijira dake gabashin Diffa a karshen mako, 'yan gudun hijiran sun nuna kosawa da mawuyacin halin da suke ciki.
Malama Zara Mustapha da ta fito daga garin Malam Fatorin Najeriya mai sheakaru 38 da haihuwa da 'ya'ya bakawai ta bayyana cewa abincin ma da zasu ci ya zama jidali a yau. Ga kuma zaman kashe wando dake damunsu saboda babu komi da zasu iya yi na samun abun hannu. Basu da sutura da zasu sa. Basu da kasuwa balantana su fita su nemo abun da zasu ci.
Malama Fanta Ari mai shekaru 55, shekaru biyu ke nan da ta gudo daga garin Barwa da 'ya'yanta hudu da jikoki shida sakamakon har haren Boko Haram. A cewarta zaman dar dar din da suke yi a sansanin nasu ya sa dole wani lokacin sukan kwana a daji. A halin yanzu basu da abincin da zasu ci ga kuma fama da rashin lafiya. Kudin sayen magani ma babu.
'Yan gudun hijiran na son a mayar dasu garuruwansu na asali tun da an soma samun sauki a garuruwan nasu.
Mataimakin sakataren, bayan da ya saurari 'yan gudun hijiran da kuma abubuwan da ya gani, ya yi alkawarin idar da sako da zara ya koma ofishinsa domin a gaggauta aika masu da tallafin da ya dace.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Facebook Forum