Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zargin Cin Hanci A Majalisar Dokokin Najeriya


Babu Wani Mutum Da Ya Bawa Majalisa Kudi Don Tayi Dokar Da Zata Cutar Da ‘Yan Najeriya: Alhassan Ado Doguwa

Majalisar Wakilan Najeriya ta nada kwamitin mutum 15 da zai yi bincike akan wani zargi da aka yi a kafafen yada labarai cewa, Kakakin Majalisar Femi Gbajabiamila ya karbi cin hanci daga kasashen waje, na dalar Amurka miliyan 10 kafin ya kawo kudurin sauya dokar rigakafin cututtuka masu yaduwa ciki har da cutar coronavirus.

Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai Alhassan Ado Doguwa a wata hira da muryar Amurka ya ce, ya kamata mutane su toshe kunnuwan su daga karairayin da ake watsawa a kafafen sada zumunta. Ya ce, kudurin dokar da majalisar ta ke kokarin kafawa karkashin jagorancin kakakin majalisar Femi Gbajabiamila akan riga kafin cututtuka masu yaduwa, za a yi shi ne don kawo ci gaban Najeriya.

Ya kara da cewa, rade-radin da ake yi na cewa wani ko wata daga kasashen waje ya ba da cin hanci domin majalisa ta kawo kudirin dokar ba gaskiya ba ne, "kuma majalisar ba za ta gabatar da duk wata doka da bazata amfani Najeriya ba" in ji chi, "babu wani mutum da ya baiwa majalisar kudi domin tayi dokar da zata cutar da ‘yan Najeriya".

Ya ce, sunyi Allah wadai da wannan rade-radin da ake yadawa, kuma majalisa za ta dauki mataki na shari’a akan masu yada wannan jita-jitar.

Saurari cikakkiyar tattaunawar da Medina Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG