Mutane da dama a Sokoto na ta fargaba bayan da aka fitar da wani rahoto mai cewa ana zargin mutum 170 da shigowa da cutar Coronavirus cikin jihar.
Rahoton wanda jaridar Daily Trust ta rawaito ya bayyana cewa hukumar dakile cututtuka ta NCDC ta karbi wani koke kan wasu jama’a da suka dawo daga wasu jihohi da ke da cutar.
Lamarin da ya tilasta wa hukumar fara gwaji kan wadannan mutanen 170.
Tun da aka samu wannan labarin dai mutane da dama a Sokoto suka fara zaman dar-dar.
Kwamishinan lafiya a jihar Alhaji Muhammadu Ali Inname, ya sheda wa Muryar Amurka cewa har yanzu ba a samu mutum ko daya da cutar ba.
Ya ce “mutane ne ke ta kira idan suka san wanda ya dawo daga wani gari, shiyasa muke ta gwada su, ba wai don mun ga wasu alamu ba.”
“Mutum 18 da muka gwada duk basu dauke da cutar,” a cewar kwamishinan.
Har yanzu dai ana ci gaba da gwada mutanen da ake zargin cewa suna dauke da cutar.
Saurari cikakken rahoton a sauti.
Facebook Forum