Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Kenya: Jami'an Tsaro Sun Yi Fade - Sun Ci Karensu Ba Babbaka


A man and a woman take a selfie under blooming Yoshino cherry trees on the edge of the Tidal Basin in Washington, D.C.
A man and a woman take a selfie under blooming Yoshino cherry trees on the edge of the Tidal Basin in Washington, D.C.

Kungiyar rajin kare hakkin dan adam ta "Human Rights Watch," ta ce jami'an tsaro sun ci karensu ba babbaka ta wajen yin fade ma mata da 'yan mata - kai har ma da maza. Wannan ko baya ne ga wasoson da kuma barnata dukiyoyin da su ka yi ta yi babu kakkautawa.

Kungiyar rajin kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch, ta ce ‘yan sandan Kenya sun yi fade ma mata da dama, tare kuma da dukar wasu fararen hula a yayin zaben Shugaban kasa na wannan shekarar.

“An yi ta aikata lalata karfi da yaji da mata da kuma ‘yan mata. Hatta maza ma ba a barsu ba,” a cewar kungiyar kare hakkin dan adam din a jiya Alhamis a wata takardar bayanin da ta fita ta bayabayan nan.

Kungiyar ta human rights watch ta ce da ita da wasu kungiyoyin na kare hakkin dana dam sun “nadi shaidar da ke nuna yadda ‘yan sanda ke amfani da karfin da ya wuce kima kan masu zangazanga, su ka yi ta kashewa da bugu da kuma murkushe mutane, da kuma wasoso da barnata dukiyoyi.” Haka zalika, an yi amfani da hanyoyin kuntatawa a harin da aka kai kan yara da kuma mazajen wadannan matan a cewar wannan rahoton.

Sufeto-Janar na ‘yansandan Kenya Joseph Boinnet ya yi watsi da rahoton da cewa ba wani abu ba ne illa “kage” ya na mai kira ga kungiyar ta Human Rights Watch da ta gabatar da hujjoji.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG