Hukumar kwallon kafa ta duniya ta mai da amsa kan wasikar da hukumar kwallon kafa ta kasar Masar ta aika mata, kan ta fito ta bayyana mata ina kuri'unta guda 5 suka shiga, a yayin zaben gwarzon dan wasan FIFA na 2019, da ya gudana a birnin Milan na kasar Italiya.
A sakon da FIFA ta fito dashi kan wannan batu da ake zarginta, tace kuri'u guda biyu da kocin kasar Masar Shawky Gharib da Kaftin din kungiyar Ahmed Elmohamady, suka jefa akwai matsala domin sun rubuta ne da manyan harrufa (Capital Letter) hakan ne yasa ba'a kidaya da su ba har ila yau ba sa hanun Sakatare na EFA.
Hukumar wasan ta kasar Masar ta ce wakilanta a wajen sun zabi dan wasan kasar ne Mohammad Salah, amman sai aka ga ba'a kirga da nasu ba, hakan ya jawo zargi da dan wasan Salah keyi wa kasar na cewar sunki zabansa.
Inda ya cire wasu hotuna daga shafinsa na sada zumunta Tweeter da ke da alaka da kasarsa.
A yayin zaben dan wasan Barcelona Lionel Messi ne ya lashe kyautar, sai Virgil Van Dijk na Liverpool a matsayi na biyu, Cristiano Ronaldo na uku daga kulob din Juventus, Mohammad Salah na Liverpool kuwa shi ya zo na hudu banda kuri'u biyu da ba'a saka suba.
Facebook Forum