Kimanin jami’an tsaro dubu 40 ne aka jibge a jihar Kogin Najeriya domin tabbatar da an gudanar da zaben gwamnan jihar lafiya da zaa yi a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba
Hukumomin tsaron Najeriya sun sha alwashin tabbatar da tsaro alokacin wannan zabe wanda ga bisa dukkan alamu yake cike da kalubale da kuma fargaba.
Zaben na jihar Kogi za a gudanar da shi ne tare da na jihohin Imo da Bayelsa da ke kudancin kasar.
Jami’an tsaron da ka tura Kogin sun hada da sojoji da ‘yan sanda da kuma Civil Defence da ma sauran masu damara tuni suka mamaye lungu da sako na jihar kogin
DIG Habu Sani daga Hedikwatar rundunar ‘yan dan Najeriya aka aika jihar ta Kogi domin tabbatar da zaben ya gudana lafiya ya kuma ce suna shirye da duk wasu ‘yan daba masu shirin kawo cikas a lokacin zaben.
Wasu ‘yan jihar Kogin sun ce za su fito kada kuri’arsu duk da cewa suna cikin zullumi kamar yadda wasu daga cikinsu suka shaidawa Muryar Amurka.
Hukumar zaben jihar Kogin dai ta ce ta gamsu da matakan tsaron da jami’an tsaron suka dauka kamar yadda kakakin hukumar Alh. Hulliru Haruna ya shaidawa Muryar Amurka.
A halin da ake ciki dai gwamnan jihar Kogin Alh.Yahaya Bello ya bukacin rundunar ‘yan sandan Najeriyar da ta gudanar da kwakkwaran bincike tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu a rikice-rikicen da suka auku lokacin yakin neman wannan zabe na ranar Asabar.
Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari:
Dandalin Mu Tattauna