Ana kwana daya da zaben gwamnonin jihohi da 'yan majalisu sai gashi a jihar Neja wasu 'yan takarar kujerar gwamnan jihar sun janye. Basu tsaya na ba sun baiwa dan takarar jam'iyyar APC goyon bayansu..
A wani taron manema labarai na hadin gwiwa 'yan takaran su uku da suka fito daga UPP da Action Alliance, da APGA sun ce sun dauki matakin ne domin marawa dan takarar kujerar gwamna na jam'iyyar APC Alhaji Habu Sani Bello baya.
Dan takarar Action Alliance Usman Shehu Sha'aibu yace sun yanke shawara ya sauka domin su goyawa APC baya. Muhammad Hassan Bida na UPP yace bayan shawarwari da suka yi sun cimma daidaito cewa dan takarar APC ya cancanta ya zama gwamna saboda a samun zaman lafiya. Shi ma Musa Aliyu Liman shugaban APGA reshen jihar Neja yace sun yi muba'aya ga Abubakar Sani Bello domin inganta dimokradiya.
Wannan lamarin wani barazana ne ga jam'iyyar PDP wadda ko a wannan makon tayi asarar wasu jigajiganta a jihar yayin da suka canza sheka zuwa APC. To saidai kakakin PDP Alhaji Hassan Saba yace abun dake faruwa alama ce ta rashin amincewa da ikon Allah. Duk wanda ya dogara ga Allah ya san lokaci ne da Allah ya kawo.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.