Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2015: Karancin Malaman Zabe a Sansanonin 'Yan Gudun Hijira, Jihar Borno


Shugaban Hukumar Zabe ta INEC Farfasa Attahiru Jega
Shugaban Hukumar Zabe ta INEC Farfasa Attahiru Jega

An samu matsalar malaman zabe da kayan zaben a sansanonin 'yan gudun hijira dake jihar Borno

Rashin samun katunan zabe na din-din-din da karancin malaman zabe da kayan aiki sun kawo cikas wa 'yan gudun hijira dake jihar Borno duk da karin kwana daya da hukumar zabe tayi.

Wasu 'yan gudun hijiran sun koka da rashin samun katunan zabe da kuma rashin isowar jami'an zabe a lokacin da suke jiransu. Wadanda basu da katunan zabe ba'a bari sun kada kuri'a ba.

Wakilin Muryar Amurka ya tuntubi kwamishanan zabe na jihar Borno akan koken 'yan gudun hijiran. Yace wasu sun bugo masa cewa malaman zabe basu isa sansanonin ba. Yace lamarin ya damesu domin sun riga sun sanar cewa sun raba kayan aiki kuma malaman sun tafi wurin zaben. Yace abun da ya jawo jinkirin shi ne wasu sun ki su bada motocinsu domin su kai jami'an zabe sansanonin. Wasu kuma sun ji tsoron tafiya da dare saboda yanayin tsaro.

Yanzu dai ana jiran sakamakon zabe ne.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG