Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Gudanar Da Zabe Mai Tarihi A Kasar Angola Cikin Watan Agusta


Zabe A Angola
Zabe A Angola

Duk da kasancewar zabe da za'ai a Angola cikin watan Agusta mai zuwa zabe ne mai dimbin tarihi, Hankalin Al'umma ya karkata ne akan makomar kamfanin Man Fetur na kasar.

Kasar Angola na shirin gudanarda wani muhimmin zabe na tarihi inda za’a ga saukar shugabanta Jose Eduardo Dos Santos da ya share shekaru 38 kan karagar mulki.

Sai dai kuma yayinda ake shirin wannan zaben, masana wainar da ake toyawa a Angola sunce hankalin duniya zai juya ne, ba a kan zaben ba, sai a kan halin da babban kampanin man petur na kasar mai suna “Sonangol” yake ciki, musamman ta fuskar abinda ya shafi kudade.

Shi kansa zaben da za’a gudanar a watan Agusta ana daukar ba wani dogon turanci ke cikinsa ba, da yake an san zabe ne a tsaakanin jam’iyyar da ta dade tana mulkin kasar da kuma jam’iyyun adawa.

Sai dai kuma an san cewa duk jam’iyyar da tayi nasara itace zata sarrafa arzikin man fetur din da Allah ya baiwa Angola, wanda a kansa ne kasar ta dogara wajen samun kudaden shiga da na gudanar da aiyukkan yau da kullum.

Yanzu abinda kowa ke tambaya akai shine: me zai faru ga kampanin na Sonangol, wanda yanzu haka yake karkashin kulawar wata mace mai suna Isabel dos Santos, wadda akace a duk Afrika ba attajira kamarta – wacce kuma ita ‘yar shugaban kasar mai ci a yanzu ne.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG