Kamfanin jirgin sama na Dana ya kare lafiyar jiragensa, a sakamakon hatsarin daya daga cikin jiragensa daya kasha dukkan fasinjoji dari da hamsin da uku.
Laraba wani baban jami’in kamfanin mai suna Francis Ogboro ya fadawa yan jarida cewa, babu yadda za’a yi injiniyan jirgin ya bari jirgin ya taso idan ya san akwai matsala.
Mai magana da yawun kamfanin Lyod na Ingila kamfani da ya baiwa kamfanin jirgin Dana inshora ya fada a jiya Laraba cewa zai biya diyan wadanda suka rasa rayukansu. A wajen wani taron yan jarida na hadin gwiwa da gwamnatin jihar Lagos aka gabatar da wannan bayani.