Yanzu haka birnin Los Ageles na jihar California shine yake kan gaba wajen samar da sabbin hanyoyin makamashin zamani na wutan lantarki, kuma jihar ta yi alkawarin za ta yi amfani da hanyoyi masu tsafta wajen samar da wutar lantarkin, ciki har da iska da kuma hasken rana nan da zuwa shekarar 2045.
Sai dai abu daya da yake musu tarnaki shine wajan ajiyar wutar, amma za su yi amfani da tsohuwar hanyar da ta hada da ruwa, watakila ta taimakawa jihar ta cimma muradinta na rage hayaki maisa dumamar yanayi zuwa matakin kauda shi baki daya.
Ana iya warware matsalar ta hanyar ‘’Samar da babban baturi” wanda zai ringa amfani da wurin ajiye ruwa a matakai daban-daban, da za’a dinga ta da shi da zai dinga kunna wutar lantarkin da kashewa da aka samar daga iska da haske rana, wanda za ta ringa samar da wutar lantarkin a lokacin da ake bukata.
Jihar California ta sakawa kanta wa’adin za ta samar da kashi 60 cikin dari na sabbin hanyoyin da za ta samar da wutar lantarkinta, zuwa shekarar 2030 da kuma yin amfani da hanyoyin gaba daya da babu hayaki zuwa shekarar 2045.
Facebook Forum