Mata na fuskantar kalubale daban-daban a Najeriya daga bangarori da dama. Sabuwar babbar Daraktar hukumar kasuwanci ta Duniya WTO Dr. Ngozi Okonjo Iweala, ta bayyana mata a kasar a matsayin jajirtattu, wadanda ke kokarin ganin an dama da su ako wane mataki, kana ta yi alkawarin tafiya da mata wajen ganin an taimaka musu inganta harkokin kasuwancinsu.
Kalaman hakan ya fito ne a yayin kammala ziyarar aiki na kwanaki hudu da Daraktar hukumar kasuwanci ta Duniya wato WTO Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, ta kawo Najeriya a karon farko tun bayan kama ragamar shugabanci na hukumar.
Wasu daga cikin ma’aikatun da ta kai ziyara har da ma’aikatar harkokin mata ta tarraya, inda babban Ministar Ma’aikatar Dame Pauline Taline ta karbi bakwancinta tare da wasu jiga jigan mata a kasar, Okonjo Iweala dai ta bayyana cewa daga cikin ayyukan hukumar, za’a taimakawa mata masu kananan sana’oi a Najeriya, wajen ganin sun inganta sana’oin su don a dama da su a matakin kasa da ma kasuwar duniya baki daya.
Ta kuma ce ta dau duk wasu bayanai da suka kamata daga bakin Ministar, mussaman wadanda suka jibanci koyar da mata harkokin kasuwarci cikin wani sabon shiri mai Taken She for Trade da kuma hanyoyin bunkasa shirin da zai tattaro mata dama.
Makasudin ziyarar tata dai shi ne su lalubo hanyoyin bunkasa harkokin kasuwanci da cinikayya, da kuma farfado da ayyukan da za su bunkasa tattalin arzikin kasar, lamarin da Babbar Mai Taimaka Wa Shugaban Kasa ta Mussaman kan Sha’anin Harkokin Mata a Najeriya, da Kuma Ayyukan da Suka Shafi Ofishin Uwargidar Shugaban Kasar, Hajiya Hajjo Sani ta ce abun alfahari ne kuma ba shakka babbar Daraktar ta hukumar ta WTO za ta yi rawar gani wajen cimma hakan.
A karshen jawabinta Okonjo Iweala, ta bayyana takaicinta dangane da sace 'ya'ya mata da wasu batagari ke yi a makarantun kasar, wanda, a cewarta hakan babban kalubale ne da ka iya zama barazana ga sha’anin neman ilimi, da karatun mata a Najeriya, ta kuma yi kira ga masu aikata wannan muggan ayyukan da su kyale yara maza da mata su nemi ilimi.
Ga rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim a cikin sauti.