Za’a gudanar da zaben ne a ranar Asabar mai zuwa, wato 25 ga watan Fabrairu, kuma zai kasance mai matukar muhimmanci, lamarin da ya sa dauki tsauraran matakan tsaro domin mazabar ce ta karshe da ta gagari a gudanar da zabe a jihar ta Rivers dake kudu maso kudancin Najeriya.
Jihar river ta yi kaurin suna wajen tashin hankalin a duk lokacin da za a gudanar da zabe
Ko a zaben watannin baya da aka yi, an kashe wani jami'in 'yan sanda mai suna DSP Alkali Muhammeda wanda aka masa kai da tare kuma da kashe jami’in da ke rufa masa baya.
Wannan zaben ya jawo rundunar 'yan sanda ta Najeriya ta damke da kuma korar shida daga cikin jami’anta dake tawagar Gwamna Ezenwo Wike da aka samu da harba bindiga kuma hakan ya jawo hargitsa a wata cibiyar zabe.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar ta INEC Nick Dazang ya bayyana cewar zamanin nadi ya shude kuma abin takaici ne ace a wannan karni har yanzu mutane na yin haka domin cimma burinsu.
Domin karin bayani sai a saurari rahoton Nasiru Adamu El-hikaya.
Facebook Forum