Najeriya da Sa'udiyya da akasarin kasashen larabawa na yankin Gulf sun bayar da sanarwar cewa za a yi Eid al-Fitr, watau sallar azumi, a ranar Jumma'a, abinda zai kawo karshen azumin watan Ramadan.
Majalisun kula da harkokin addini a Sa'udiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa, da Kuwait da wasu kasashen na larabawa sun ce ba a ga sabon wata ba a bayan faduwar rana jiya laraba, ma'ana za a kara azumi guda daya kafin a yi Sallar Eid.
Daga Najeriya ma, sanarwar da ta fito fadar Sarkin Musulmi ta ce ba a samu rahoton da ya cika ka'idar shari'a ta ganin wata ba, saboda haka za a yi azumi talatin a bana. Wannan shi ne karon farko cikin shekaru kimanin 30 da ake cika azumi 30 a kasar.
Ganin wata ko yanke shawarar farawa ko kawo karshen azumi yana bambanta daga kasa zuwa kasa. A Jamhuriyar Nijar, an ba da sanarwar ganin wata, kuma ana sallar azumi a yau alhamis a can.
Azumin watan Ramadan yana daya daga cikin shika-shikan Musulunci guda biyar.