Babban gidan ajiyar namun daji ‘Zoo’ na tsakiyar birnin Mexico ‘Chapultepec’ na cike da farin ciki da kuma fara shirye-shiryen bukin radin suna, na jaririn Rakumin Dawa da aka haifar musu na biyu a cikin wannan shekarar, wanda ake kira “Giraffe” a turance.
Jaririn rakumin da aka haifa wanda tsawon shi ya kai na cikakken mutum, kimanin makonni kadan kamun haihuwar jaririn, aka kwantar da mahaifiyar sa, don ba ta kulawa na musamman.
Ya zuwa yanzu dai an fara sauraran ra’ayoyin jama’a don zaben wane suna za’a radawa jaririn.
A cewar shugaban gidan Zoo din Juan Carlos, gidan Zoo din mai shekaru 96 da kafawa, na da namun dawa iri daban-daban, a cikin wannan shekarar kawai sun samun karuwa na haihuwar sauran na’ukkan namun daji da suka kai 170.
“Haihuwar Rakumin dawa wani abin ban sha’awa ne ga wannan gidan namu.” Domin kuwa yanzu haka ana samun karancin na’ukkansu a fadin duniya.
Tun a karni na 17 aka fara fuskantar raguwar jinsin na Rakumin dawa a nahiyar Afrika, wanda a nahiyar ce suka fi yawa.
Ana sa ran Rakuman biyu da aka haifa a cikin wannan shekarar 2019, za su samu kulawa ta musamman, su kuma gudanar da rayuwarsu kamar kowa a cikin gidan a cewar shugaban gidan Mr. Juan.
Facebook Forum