Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za a yi amfani da hotunan Nelson Mandela a takardun kudin Afrika ta Kudu


Sababbin takardun Kudin Afrika ta Kudu
Sababbin takardun Kudin Afrika ta Kudu

Afrika ta kudu ta kaddamar da wadansu sababbin takardun kudi dake dauke da hoton tsohon shugaban kasar Nelson Mandela.

Afrika ta kudu ta kaddamar da wadansu sababbin takardun kudi dake dauke da hoton tsohon shugaban kasar Nelson Mandela.

Shugaba Jacob Zuma ne ya sanar da haka jiya Asabar yayin bukin cika shekaru 22 da sakin Mr. Mandela daga kurkuku bayan ya shafe kusan shekaru 30 yana daure sabili da gwaggwarmayar da ya yi lokacin yaki da wariyar launin fata.

Sababbin takardun kudin biyar na kudin da ake amfani da shi a Afrika ta kudu da ake kira rand sun kunshi rand 10, 20,50,100 da kuma 200, wanda aka buga da nufin karrama Mr. Mandela a matsayin shugaban kasar bakin fata na farko da aka zaba karkashin tsarin damokaradiya a cikin shekara ta dubu da dari tara da casa’in da hudu. Nelson Mandela dan shekaru 93 wanda yake fama da lauyayi bai halarci bukin kaddamar da kudin da aka gudanar jiya asabar ba. Tsohon shugaban kasar da ya sami lambar yabo ta Nobel bai cika fita bainin jama’a ba yanzu.

Ana kyautata zaton za a fara amfani da takardun kudin dake dauke da hotonshi karshen wannan shekarar.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG