Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Gudanar Da Zaben Farko Tun Bayan Mugabe A Zimbabwe

Shugaba Emmerson Mnangagwa, a dama, yana gaisawa da jagoran 'yan adawar kasar, Morgan Tsvangirai, a lokacin da ya ziyarci madugun a gidansa dake Harare, Jan. 5, 2018.
Shugaba Emmerson Mnangagwa, a dama, yana gaisawa da jagoran 'yan adawar kasar, Morgan Tsvangirai, a lokacin da ya ziyarci madugun a gidansa dake Harare, Jan. 5, 2018.

Shugaban Zimbabwe Emerson Mnangagwa ya ce za’a gudanar da zabe a kasar nan da watani 4 zuwa 5, zabe na farko tun baya da aka hambarar da dadadden shugaban kasar Robert Mugabe.

Shugaban Zimbabwe Emerson Mnangagwa ya ce za’a gudanar da zabe a kasar nan da watani 4 zuwa 5, zabe na farko tun baya da aka hambarar da dadadden shugaban kasar Robert Mugabe.

Mnangagwa ya yi wannan alkawarin jiya Laraba yayin wata ziyarar aiki da ya kai Mozambique, makwabciyar kasarsa, a cewar jaridar Herald ta gwamnatin kasar

Dole ne mu yi ta yayata samun zaman lafiya a cewar shugaban Zimbabwe lokacin da yake bada sanarwar yin zaben. Ya yi alkawarin zai tabbatar an gudanar da zabe cikin 'yanci da adalci domin tabbatar da cewar Zimbabwe ta shiga jerin kasashen da suka chanchanci Dimokuradiyya. “Ana sa ran yin zaben a watan Yuli ko Agusta."

Tsohon shugaba Mugabe dan shekarar 93 ya yi mulki a Zimbabwe na tsawon shekaru 37 kafin aka tilasta masa sauka daga mulki a watan Nuwambar bara bayan da sojoji suka yi masa juyin mulki kuma ya yi hasarar goyon bayan 'yan Majalisar dokokin kasar, yan jamiyar ZANU-PF da ke mulki.

Lokacin tsawon mulkin Mugabe a Zimbabwe, zabubbukan da aka gudanar a kasar sun fuskanci magudi da tarzoma.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG