Gungun masu bin kadin shari’a a Jihar Kansas a nan Amurka sun fara yin muhawara kan shari’ar wani tsoho tukuf da ake zargin yana da hannu a a kashe-kashen kare-dangin da aka yi a Rwanda shekaru 17 da suka shige.
Jiya laraba lauyoyi masu gabatar da kara da masu kare Lazare Kobagaya suka kammala gabatar da jwabansu na karshe a wannan shari’a. Ana tuhumar Kobagaya mai shekaru 84 da haihuwa da laifin yin karya game da tarihin rayuwarsa ga jami’an shige da ficen baki na Amurka a lokacin da ya nemi takardar zama dan kasa a 2006.
Masu gabatar da kararraki sun ce a takardun da ya cike na neman zama dan kasa, yayi ikirarin cewa yana zaune ne a kasar Burundi a lokacin kisan kare dangin na 1994 a Rwanda, ya kuma ce bai taba aikata wani laifi ba.
Masu gabatar da kara sun ce Kobagaya, dan kabilar Hutu, ya bayarda umurnin kashe makwabtansa ‘yan kabilar Tutsi a kauyensu mai suna Birambo, ya kuma kitsa wani harin da ya kashe dubban Tutsawa dake tserewa a wani tsauni dake kusa da nan.
Lauyoyin kariya suka ce Kobagaya ba haka yake ba, kuma a lokacin kashe-kashen ma ya taimaka wajen ceton ran matarsa ‘yar kabilar Tutsi. Lauyoyin suka ce wasu mutanen kauyen dake da hannu a kashe-kashen ne suka shafa ma Kobagaya kashin kaji a saboda a rage musu hukumce-hukumcen da aka yanke musu.
Idan an samu Kobagaya da laifi, to ana iya korarsa daga nan Amurka a maida shi kasar Rwanda.