Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
Afirka

Za a Fara Horas Da 'Yan Jarida a Nijar Gabanin Zabe


Wani taron hukumar zabe da aka yi a baya.
Wani taron hukumar zabe da aka yi a baya.

A Jamhuriyar Nijar an shirya wani taro domin ganar da matasan ‘yan jarida dubarun kaucewa fadawa tarkon masu yada bayanan bogi a kafafen sada zumunta musamman a wannan lokaci da ake shirye-shiryen zaben gama gari a kasar.

Kungiyar Renjed mai fafutukar samar da ci gaban kasa da tallafin Oxfam da masarautar Danemark ne suka shirya wannan taron.

Sanin rawar da kafafen yada labarai ke takawa akan maganar wanzar da zaman lafiya da kuma irin hadarin da ke tattare da aikin jarida a wannan lokaci da kafafen sada zumunta ke kara daukar hankalin jama’a ya sa kungiyar Renjed shirya wannan taro.

Babban burinsu shi ne gwada wa matasan ‘yan jarida dabarun kauce wa fadawa tarkon masu yada labarun bogi kamar yadda shugabanta Ousman Dambaji ya shaida wa Muryar Amurka.

"Yanzu lokacin zabe ya kusan isowa. Shi yasa muka ga ya kamata mu koya wa 'yan jarida yadda ake tantance labaran gaskiya. Hakan zai hana wasu 'yan siyasa yi wa juna kazafi."

Shugaban hukumar zabe ta CENI Me Issaka Sounna da babban jami’in shiga tsakanin na kasa Me Ali Sirfi Maiga sun halarci bukin bude wannan taro na hadin gwiwar Renjed da masarautar Danemark.

Yada labaran bogi kan shafukan sada zumunta wata babbar matsala ce wacce ke addabar duniya gaba daya, lamarin da kan janyo sauya sakamakon zabe a wasu kasashen.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG