Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za a fara amfani da wata sabuwar na’urar gwada cutar kanjamau


Wani maganin cutar kanjamau
Wani maganin cutar kanjamau

Hukumar tantance inganci abinci da magunguna ta Amurka ta amince da amfani da wata sabuwar na’urar gwada kwayar cutar kanjamau

Hukumar tantance inganci abinci da magunguna ta Amurka ta amince da amfani da wata sabuwar na’urar gwada kwayar cutar kanjamau, wadda mutum zai iya saya ya gwada kanshi a gida ya kuma sami sakamakon nan take.

Wannan salon gwajin da ake kira “OraQuick”, ana amfani da shi ne, ta wajen share dasashen hakori da tsinken dake dauke da magani daga nan a sa cikin kwalbar gwaji wadda zata nuna ko mutum yana dauke da kwayar cutar ko babu cikin mintoci 20.

Idan sakamakon ya nuna cewa, mutum yana dauke da kwayar cutar kanjamau, ana bukatarshi ya tafi wajen likita domin sake yin gwajin da zai tabbatar da sakamakon na farko.

Hukumar ta amince da amfani da na’urar ne wadda za a iya saye a kemis, bayan watanni biyu da wani kwamitin mashawarta mai membobi 17 ya kada kuri’ar amincewa da amfani da na’urar.

Duk da yake kwararru suna cewa, babu tabbas a sakamakon da wannan na’urar zata bayar, hukumar ta bayyana cewa, illar rashin sanin kamuwa da cutar yafi muni kasancewa gwajin zai iza mutum tuntubar likita domin neman tabbacin ko yana dauke da cutar ko babu..

Dr. Nitika Pant Pai,Wani farfesar magani ta jami’ar Montreal's McGill , ta bayyana cewa, saida na’urar a kemis ba tare da neman izinin likita ba, zai rage dari- dari da kyamar da ake yi da zuwa gwajin kwayar cutar HIV.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG