Mutane dake cin kasuwar suna sayar da kifi da sauran kayan miya irin dangin su ganyen miya da tumaturi da albasa da dai sauransu.
Wadan da aka tambaya cikin masu sayar da kaya a kasuwar sun ce basu san yadda zasu yi ba domin sun dade suna sayar da kayansu haka nan shekara da shekaru babu abun da ya samesu kuma babu wanda ya kawo masu kuka.
Shi ma wani mai sayar da tsire gaf da bakin inda aka tara dimbin shara yace ya san wurin nada kazanta da dama sai dai a taimaka masu domin ciniki ya ragu saboda halin kazanta.
Wata da ta zo sayen kayan abinci tace suna tsoro amma babu yadda zasu yi. Suna son gwamnati ta dauki mataki.
Wani likita Bala Haruna da aka tambayeshi ko sayar da abinci cikin mummunan kazanta ka iya haifar da wani annobar cutututa sai yace sun yi bincike kuma sun gano wasu na kamuwa da ciwo saboda kazanta a wuraren sayar da abinci.
Ga rahoton Garba Lawal da karin bayani.