Su ma tsuntsaye akan sami masu fama da matsalar kiba, wadda rageta ka iya zama babbar matsala.
Wata cibiyar kare hakkin namun daji da bada agaji a Burtaniya, ta ce wata Mujiya wacce aka tsinta a wani rami a farkon watan Janairu, da ake kyautata zaton cewa ta ji rauni ne, sai daga baya aka gano cewa tana fama ne da matsalar "muguwar kiba."
Kungiyar ta Suffolk Owl Sanctuary dake gabashin Ingila ta fada wa gidan talabijin na NBC News a ranar Alhamis cewa wani jami'in kungiyar ne ya tsinto Mujiyar.
Lokacin da jami'an asibitin dabbobin suka yi gwaje-gwaje suka kuma auna nauyin wannan mujiyar, sun gano cewa ta na da nauyi sosai kimanin gram 245, a cewar kafofin yada labaran kungiyar.
Wannan kusan ita ce Mujiya ta ukku da aka gani da ta fi babbar lafiyayyar tsuntsuwa nauyi sosai. Nauyin ta ya sa ba ta iya tashi da kyau saboda yawan kitsen dake jikinta.
Kamar yadda ba kasafai ake ganin tsuntsaye a cikin wannan yanayin ba, masu kula da tsuntsayen daji sun yanke shawarar su lura da Mujiyar har tsawon makonni don ganin dalilin da yasa ta ke kiba.
Facebook Forum