Amurkawa na nan sun kagara, marecen yau yazo lokacinda za’a gwabza a muhawarar farko daga cikin muhawarori ukku da za’a fafata tsakanin shugaba Barack Obama da abokin takararsa a zaben shugaban kasa na bana na jam’iyyar adawa ta ‘yan Republicans, Mitt Romney.
Yanzu, da makkoni biyar kafin ayi zaben da za’yi ran 6 ga watan Nuwamba, Shugaba Obama zai je wannan muhawara yayinda yake a gaban Mr. Romeny a tagomashin jama’a a kasa baki daya da kuma a irin jihohin nan da akance “sai an ja daga” wadanda kuma akance duk wanda ya lashe su, shine zai zama shago mai cinye zaben.
Shi dai Mr. Romney wanda hamshakin attajiri ne kuma tsohon gwamnan jihar masachusetts, ya yi bakin jini tun lokacinda wasu magangannun da yayi, da ya zaci a cikin asiri yayi su, suka bulla inda kuma aka ji shi yana gayawa wa attajirai ‘yanuwansa masu tara mishi kuddin tabaccin cewa ai kashi 47% na mutanen Amurka da zasu jefawa shugaba Obama kuri’unsu, duk mutane ne da basa biyan haraji, kuma wadanda ke jin dole gwamnati ta basu tallafin rayuwa.
A yau shugaba Obama da shi Mr. Romney din duk sun kulle kansu, suna ta harda da da gwajin wannan muhawara da mukarabbansu.