Kusan mutane milyan biyar ne wadanda aka yiwa rijista suka tafi rumfunan zabe yau Lahadi, a jamhuryar Benin dake Afirka ta yamma, domin su kada kuri'unsu a zaben shugaban kasa.
Mutane 33 ne suke takara domin su gaji shugaba Thomas Boni Yayi. Zai bar kujerarsa ce bayanda ya cika wa'adin da tsarin mulkin kasar ya kayyade na wa'adi biyu. Al'amari dake kara karfafa kallon da ake yiwa kasar a zaman abar koyi ta fuskar demokuradiyya, a nahiyar dake fama da matsalar shugabannin da suke ta kwaskwarima ga tsarin mulkin kasshensu, domin su dawwama kan mulki.
Shugaba Boni Yayi ya gayawa manema labarai lokacinda yake kada tasa kuri'ar cewa, zai mikawa magajinsa kasa wacce kanta yake a hade.
Cikin 'yan takarar harda PM Lionel Zinsou, wanda shugaba Boni Yayi da jam'iyyar da take mulki suke marawa baya, da Patrice Talon, wani hamshakin attajiri, wanda ya kudance ta cinikin auduga, babbar abunda kasar Benin take samun kudin akai a kasuwannin ketare.
Zinsou yana shan suka saboda danganatakarsa da kasar faransa inda aka haifeshi kuma ma yafi dadewa a can.
Idan babu dan takara wanda ya lashe zaben kai tsaye, za'a yi zaben fidda gwani, mako biyu bayan kammala zaben na yau.