Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ta Ke Ranar Mata Ta Duniya Baki Daya


 Wasu mata a Mozambique
Wasu mata a Mozambique

Yayin da mata a fadin duniya, musamman ma a wurare irin arewa maso gabashin Najeriya ke takaicin irin cin zarafi da danniyar da ake nuna masu, yau a fadin duniya ana harkokin jaddada zagayowar ranar mata ta duniya.

Yau ta ke Ranar Mata ta Duniya, don haka a fadin duniya mata da magoya bayansu irin kungiyoyin rajin ‘yancin dan adam na ta harkokin jaddada muhimmancin mata da kuma gangami da zanga-zangar nemar a kawo karshen danniya da kwara da kuma gallazawar da mata ke fuskanta kullu yaumin.

Wannan ranar na zuwa ne yayin da ake cigaba da juyayin wani al’amari shigen wanda ya faru shekarun baya na sace daruruwan dalibai mata a garin Chibop. To saidai wannan karon dalibai mata wajen 100 ne ‘kawai’ aka sace a garin Dapchi, wanda, kamar Chibok, shi ma Dapchi arewa maso gabashin Najeriya ya ke; to amma a jahar Yobe; ba a jahar Borno, inda Chipok ya ke ba.

Yankin na arewa maso gabashin Najeriya dai ya zama turmin tsakar gida sha luguden Boko haram.

Matsalolin da ke gallabar mata sun bambanta daga kasa zuwa kasa kuma daga wuri zuwa wuri. Don haka yau sai gangami ake ta yi a kasashen duniya. Alal misali, a Manila, babban birnin kasar Filifinu (Philippine) daruruwan mata sun saka suturu masu launin jaja-jaja da akan alakanta da mata su ka bazu kan tituna don zanga-zangar nuna rashin amincewa da kisan mutane wajen 4,000 da gwamnatin Shugaba Rodrigo Duterte ta yi a yakin da ta ke yi da muggan kwayoyi. Abin da su ka ce na shafar iyali.

Kungiyoyin rajin ‘yancin dan adam sun ce nacin Shugaba Duterte na hallaka dubban dillalan miyagun kwayoyi ya sa ‘yan sanda sun shiga karkashe wadanda ake kyautata zaton dillalan miyagun kwayoyin ne ba tare da cikakken bincike ba.

A Seoul, babban birnin Koriya Ta Kudu, kungiyoyin mata sun yi amfani da wannan ranar wajen yada wata yekuwar kare mata daga masu lalata da mata ba da amincewarsu ba, wadda ake kira gwagwarmayar “Me Too.” Wannan yekuwar ta yadu a wannan babbar kasa ta Asiya bayan da a cikin watan Janairu wata lauya mace ta bayyana cewa abokan aikinta maza sun sha mata iskanci cikin shekarun da su ka gabata.

Mata a sauran sassan duniya na ta gangami saboda dalilai iri-iri masu nasaba da musguna ma mata da ake yi.

To a wani bangaren kuma ana nan ana kokarin shawo kan lamarin. Ko a jiya dinnan a nan Amurka sai da ‘yan Majalisar Dokoki su ka gana da wasu daga cikin ‘yan matan da Boko Haram su ka sace a arewa maso gabashin Najeriya don ji kai tsaye daga garesu.

Daga Nijar, ga wakilinmu da misalign yadda wannan rana ta kasance a Afirka:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

Facebook Forum

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG