Bikin ya wakana a garin Cintabara cikin jihar Tawa inda aka soma tawayen kusan shekaru 27 da suka gabata.
Wani dan jarida Malam Sidi Muhammad da ya kasance wurin bikin shi ya bada karin bayani. Yana mai cewa tun jiya da Firayim Ministan kasar ya iso suka soma bikin kafin su kammala yau, wadda kuma ta kasance ranar hutu a duk fadin kasar saboda bikin.
Yace an yi bikin cikin kwanciyar hankali da yadda ya kamata a yi.
Cikin abubuwan da Firayim Ministan yace sun hada da cewa babu wani banbanci tsakanin 'yan kasar saboda duk an zama tsintsiya madaurinki daya.
Ga rahoton Haruna Maman Bako da karin bayani.
Facebook Forum