Yayinda yake amsa tambayoyin manema labaru jim kadan bayan ya kammala zagayen ganin irin ayyukan dake gudana a filin jirgin saman na Kaduna, Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo yace kammala duka ayyuka kafin Laraba ba lallai ne ya yiwu ba amma an umarci duka 'yan kwangila su kara kaimi.
Duk da haka shugaban hukumar kula da filin jiragen saman Najeriya Injiniya Sale Binoma yace jiragen zasu cigaba da soma fara tashi da sauka a ranar Laraba domin ko dama can suna yin hakan saidai za'a cigaba da gyare-gyare.
Dangane da matakan da gwamnati ke dauka domin jin dadin fasinjoji a filin na Kaduna Injiniya Sale Binoma cewa yayi "gwamnati ta shirya sha'anin tsaro ma wadanda zasu tashi daga Kaduna su tafi Abuja walau ta mota ko ta jirgin kasa an gyara hanyoyi an kuma sa jami'an tsaro. Shi ma filin jirgin an kara jami'an tsaro saboda haka duk a shirye muke"
To ko wane irin matakan tsaro rundunar 'yansandan Najeriya ke dauka domin tabbatar da cewa ba'a samu matsala ba, Alhaji Ibrahim Idris babban sifeton 'yansandan yayi karin bayani.Yace duk fannonin 'yansanda za'a gansu a filin jirgin. A kan hanya kuma koina akwai 'yansanda. Har wa yau zasu kara 'yansandan su kara da motoci har tare da jirgi mai saukan angulu.
Su ma al'umma mazauna kusa da filin sun tofa albarkacin bakinsu. Alhaji Abubakar Hayatu yana kasuwanci ne a harabar filin jirgin saman. Yace duk da cewa an koresu daga shagunansu amma tunda maganar cigaba ce sun yi murna. Dangane da tsaro sun ce sun ga sauyi.
Ga rahoton Isa Lawal Ikara da karin bayani.
Facebook Forum