Mai martaba sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na biyu ya ja hankalin Kanawa game da ziyarar da shugaban na najeriya zai fara a yau inda ya tunashesu da halayan kwarai da aka sansu da shi.
Tuni dai talakawan Kanon suka fara bayyana ra’ayoyi mabanbanta dangane da wannan ziyarar ta Shugaba Muhammad Buhari wadda ita ce ta farko da zai kai jihar da tafi kowace bashi kuri’u lokacin zabensa. Wani cewa ya yi ko a bakin kofar gidansu aka yi gangamin tarban shugaban shi ba zai fito ba saboda maimakon a ga wuta a makera sai gata a masaka. A cewarsa duk wurin sana’o’insu sun durkushe sai mutane ake gani a zube kamar barin mota saboda rashin abun yi.
Ziyarar na zuwa ne a dai dai lokacin da Kanawa ke korafin cewa, shugaban ya yi watsi da su duk kuwa da gagarumar gudummawar da suka cewa sun dinga bashi tun lokacin da ya shiga harkokin siyasa shekaru 15 da suka gaba.
Hakan ta sanya masu fashin baki kokwanto ko siyarar shugaban ta aikin gwamnati ce ko kuma ta neman kuri’a ce
Dr Saidu Ahmad Dukawa wani masanin kimiyyar siyasa a Jami’ar Bayero Kano, injishi da dawuri shugaban ya kai ziyararsa da za’a ce ta aiki ce, amma yanzu ta fi kama da ta siyasa. Sai dai a ganisa lamarin bai hana gwamnatin Kano mika masa kokon barar neman gwamnatin tarayya ta yiwa jihar wasu manyan ayyuka ba
A makon jiya ne dai a yayin ziyara a birnin Abidjan na Ivory Coast shugaba Buhari ya yi wasu kalamai dake nuna sha’awarsa ta sake neman shugabancin Najeriya a shekara ta 2019.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani
Facebook Forum