Yau laraba al’ummar Afirka ta Kudu ke zaben majalisun kananan hukumomi, zaben da ake ganin shine Zakaran Gwajin dafin da zai nuna farin jinin jam’iyyar ANC dake mulkin Afirka ta kudun.
Ana kyautata cewar jam’iyyar ANC ce zata lashe mafi yawan kujerun majalisun kananan hukumomin, amma ana yawaita zargin jam’iyyar ta ANC da yin magudi da cin hanci da karbar rashawa.
Sakamakon kididdigar jin ra’ayin jama’ar da aka gudanar kafin zaben, ta nuna cewa babbar jam’iyyar hamayya ta D-A-P zata taka muhimmiyar rawa a zaben na yau fiye da zaben da aka gudanar a shekarar 2006. ‘Yan Afirka ta kudu sama da miliyan 23 ne suka yi rajista domin zaben na yau laraba a Afirka ta kudu.