Yau ce kasar Ghana ke bikin cika shekaru 61 da samun 'yancin kai daga turawan Ingila da suka yi mata mulkin mallaka.
Shugaban kasar na farko Dr Kwame Nkurma a ranar samun 'yancin kan ya ce kasar ta samu 'yanci har na illamasha allahu sai dai ya kara da cewa 'yancin Ghana ba zai yi tasiri ba sai sauran kasashen Afirka sun samu tasu 'yancin tare da walwala.
Kamar yadda aka saba za'a yi paretin jami'an tsaro a dandalin 'yancin kai dake babban birnin kasar, wato Accra.
Wasu shugabannin kasashen Afirka da suka hada da Shugaban Tarayyar Najeriya Muhammad Buhari, zasu halarci taron bikin. Shugaban Najeriya shi ne ma babban bako mai jawabi.
Farfesa Usman Bali ya ba Muryar Amurka takaitacen tarihin gwagwarmayar samun 'yancin kai a kasar. A cewarsa ba cikin ruwan sanyi turawan mulkin mallaka suka mika mulki ba sai da aka yi fafutika da dama. Tun shekarar 1947 aka kafa jam'iyyar siyasa ta neman 'yanci. Wasu jam'iyyun sun biyo baya har aka samu 'yancin kai.
Baicin Dr Kwame Nkurma Farfesa Usman ya ambaci wasu da suka yi ruwa da tsaki wajen kwatowa kasar 'yanci kamar irinsu Dr. Danquah da Akufo Adoo da dai sauransu.
A saurari rahoton Ridwan Abbas da karin bayani
Facebook Forum