Yau, 22 ga watan Maris, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware saboda a maida hankalin kan albarkatun ruwa da kuma batun samar da tsabtatattcen ruwa a sassa dabam-dabam na duniya. Taken ranar ruwan bana shi ne “Nature for Water,” wato amfani da hanyoyin asali wajen samar da ruwa da kuma tattalinsa.
A Najeriya da Nijar, kamar a sauran kasashen duniya, an gudanar da hidimomin jaddada muhimmancin wannan ranar. A Najeriya, wani dan Indiya wanda ya kware wajen samar da ruwa a kasashe masu tasowa, ya ce a yanzu ruwan da kan gudana a Najeriya gurbatacce ne ta yadda hakan kan haddasa cututtuka. Hasali ma, in ji shi, sama da kashi 70% na wadanda ke jinya a asibitocin Najeriya, ta ruwa su ka kamu da cututtukan. Wasu mazuna birnin Lagos na Najeriya sun koka kan rashin lafiyayyen ruwa, kamar yadda wakilinmu Babangida Jibrin ya ruwaito.
A Janhuriyar Nijar, wasu mata masu jan ruwan rijiya a wani kauye mai suna Bazaga sun gaya ma wakilin Sashin Hausa Haruna Mamman Bako cewa su na fama sosai kafin su samu ruwa; kuma idan ma an sami ruwan, ba kasafai ya ke da tsabta ba. Su ka ce ruwan da su kan ja daga rijiyar na kunshe da gasussuka da kwari da sauran yanayoyi na gurbacewa. Su na masu kiran da hukumomi su tanadar masu da ruwa.
Daga Najeriya, ga wakilinmu Babangida Jibrin da cikakken rahoton:
Daga Janhuriyar Nijar kuma ga wakilinmu Haruna Bako da cikakken rahotonsa:
Facebook Forum