Kusan kwanaki uku da suka gabata aka dawo da 'yan Najeriya 400 daga kasar Libya sanadiyar taimakon kungiyar Tarayyar Turai da wata kungiya mai kula da harkokin 'yan gudun hijira.
Yau Jumma'a kungiyoyin sun taimaka wasu 'yan Najeriyan 164 sun dawo daga Libya.
Jami'in dake kula da shiyar yammacin Najeriya na hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya, Alhaji Suleiman Yakubu shi ya fitar da sanarwar cewa akwai maza 155 cikin wadanda suka dawo da mata biyar sai kuma kananan yara hudu.
Wani Emmanuel Keshi, dan asalin jihar Delta, ya na daya daga cikin wadanda suka dawo, ya ce Libya ba kasar zuwa ba ce domin akwai azaba. Ya gargadi duk wani dan Najeriya dake sha'awar zuwa kasar ya kiyayi yin hakan. Ya ce akwai aikin yi a Najeriya saboda haka matasa su zauna gida domin gina kansu da kasarsu tare da kaucewa shiga tarkon Libya.
Inji Keshi akwai dubban 'yan Najeriya dake zaune cikin gidajen kaso a Libya kuma basu san halin da suke ciki ba. Ya ce yawancinsu sun mutu a gidajen kason.
Kimanin shekara guda ke nan da Najeriya take kokarin dawo da 'yan kasar daga Libya amma sai 'yan kwanakin nan aka zafafa dawo dasu biyo bayan taron da shugabannin Afirka da na Turai suka yi a kasar Ivory Coast.
Alhaji Abu Dansudu, daya daga cikin shugabannin 'yan arewacin Najeriya yana ganin bayan daukan matakin dawo da 'yan Najeriya daga Libya kamata ya yi gwamnonin jihohi su dauki wasu matakan na zakulo wadanda suke da hannu a cinikin bayi da safarar mutane zuwa kasar Libya da tarayyar Turai domin a hukumtasu.
Kawo yanzu an dawo da 'yan Najeriya kimanin dubu shida daga Libya cikin shekara guda.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.
Facebook Forum