Yarima Mohammed bin Salman na Saudiyya ya kawo ziyara Amurka don tallata shirinsa na sauya fasalin kasar inda ake sa ran Shugaba Trump zai karbe shi da hannun bi-biyu.
Shafin yanar gizon gidan talbijin na CNBC da ke Amurka, da kuma na Aljezeera sun ruwaito cewa, Yarima Salman zai gana da shugabannin siyasa da manyan 'yan kasuwa.
Wannan ita ce ziyararsa ta farko a nan Amurka tun bayan da aka nada shi a matsayin Yarima kamar yadda kafafen yada labaran suka ruwaito.
Shugaba Trump ya kan fito fili don nuna goyon baya ga masaurautar ta Saudiyya, wacce ke bin mazhabar Sunni a maimakon Iran da suka kasance 'yan shi'a.
Bayanai sun yi nuni da cewa Yariman, wanda aka fi sani da ‘MBS’ ya matsu don ganin kasarsa ta amfana da wannan matsayi na Trump.
A wata hira da ya yi da Tashar CBS a baya, Yariman ya kwatanta shugaban Iran a matsayin Hitler kuma ya ce muddin Iran ta mallaki makamin nukiliya to nan take Saudiyya ita ma za ta bi sahu.
“Saudi Arabia ba ta da niyyar mallakar makamin nukiliya amma muddin Iran ta kera makamin to mu ma za mu gaggauta bin sahu,” inji shi.
Dama dai shugaba Trump yana nuna shakku kan ingancin yarjejeniyar ta Iran wacce aka kulla tsakanin kasar ta Iran a bangare guda da kuma Amurka da wasu manyan kasashen duniya biyar a daya gefen.
“Suna da wasu damuwa kan yarjejeniyar nukiliya da Iran amma suna goyon bayanta in har za ta taka musu birki wajen kera makamin nukiliya,” in wani mai tsokaci na Mujallar Arab News, Fahed Nazer.
MBS yana jagorantar shirin kawo sauyi a zamantakewa ciki har da bai wa mata damar tuka mota da halartar wasannin kwallon kafa a kasar ta Saudiyya.
Zamanantar da kasar mai ra’ayin mazan jiya, na daga cikin sauye-sauyen da ya ke kokarin yi da kuma kirkiro sabbin hanyoyi masu dorewa domin inganta tattalin arzikin kasar.
Kalubalen Da Ke Gaban Yarima Salman
Sai dai kokarin da Yarima Salman ke yi na jawo masu zuba hannun jari daga waje zuwa kasar ta Saudiyya na iya fuskantar matsaloli.
A watan Nuwambar da ya gabata ne, Yariman ya sa aka tsare ‘yan kasar sama da 200 wadanda suka hada da jami’an gwamnati da attajiran Saudiyya.
Wannan mataki ya sha suka daga sassan duniya, inda kungiyoyin kare hakkin bil adama suka yi ta suka.
Sai dai Yariman ya ce daukan wannan matakin ya zama dole don yaki da matsalar almundahana kan kudaden kasa.
Amma wasu da dama na ganin mataki ne na kawar da abokan hamayyarsa.
“Suna neman masu zuba hannun jari amma me zai sa mutum ya zuba kudadensa inda babu tabbas wato gwamnati ta na iya shigowa ko yaushe ta tarwatsa komai?” inji Adreas Krieg na Kwalejin King’s a Landan.
Sannan wani kalubale, da MBS ka iya fuskanta su ne, yakin Yemen da dakarun Saudiyya ke jagoranta, wanda Amurka ke marawa baya.
Saudiyyan da Amurka na yaki ne da ‘yan tawayen Houthi da Iran ke marawa baya.
Yakin na Yemen ya haddasa mutuwar daruruwan mutane da kuma barnata dukiyoyi a kasar wacce al'umarta ke fama da matsalar talauci.
Facebook Forum