A ranar Asabar 18 ga watan Yuli, wani abu mai kama da nakiya ta fashe har wasu yara su 6 suka mutu a garin Malumfashi da ke jihar katsina a arewacin Nigeria.
Wani wanda ya shaida lamarin da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce a wata gona aka ajiye nakiyar a kusa da wani gidan kaji a garin ‘Yammama da ke karamar hukumar Malamfashi. Ana kyautata zato mai gonar, Malam Hussaini mai kwai, aka auna saboda ya kan je ya huta a wani bangaren gonar, a cewarsa.
Ya kuma ce wasu yara su 11 da suka je ciyawa a gonar, daya daga cikinsu da ta ga kunshin nakiyar ta kuma dauka bayan ta kira sauran yaran su zo su gani, a lokacin ne nakiyar ta fashe.
Mutumin da ya shaida lamarin ya kara da cewa nan take 5 daga cikin yaran suka mutu daga bisani kuma daya ya mutu a asibiti yayin da 5 suka jikkata aka kuma kai su asibitin gwamnatin garin Malumfashi. Babu wanda ya ga wanda/wadanda suka ajiye bom din saboda wani lamari ne da ba a zata ba, a cewarsa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina Superintendent Gambo Isah, ya tabbatar da aukuwar lamarin wanda ya bayyana a matsayin “abin takaici.” Ya kuma ce ko da ya ke ba a san musabbabin harin ba a yanzu, masana a fannin bom da ake kira EOD a takaice da masu bincike da ake kira CID a takaice na kan gudanar da bincike.
Batun tsaro dai wani abu ne da jihar Katsina ke fama shi, amma wannan al’amarin shi ne irinsa na farko da aka taba samu a jihar.
Saurari cikakken rahoton Sani Shu’aibu Malumfashi.
Facebook Forum